Sojan Somalia ya harbe abokanan aikinsa 5 – DW – 02/11/2024Sojan wanda rahotanni ke cewar ya bude wutar ne a yayin da sojojin ke salla, sai dai nan take aka harbe shi a wani mataki na kariya.

Ya zuwa yanzu babu masaniya a kan dalilan kai wannan harin da sojan ya yi a kan abokan aikinsa, sai dai tuni kungiya kungiyar Al-shabab da ke gwagwarmaya da makamai wacce kuma ke da alaka da da kungiyar Al-Qaeda da ta jima tana kadammar da hare-hare a kan jami’an gwamnati sama da shekaru 15 ta dauki alhakin harin.

Mahukunta a Hadaddiyar Daular Larabawa sun yi Allah wadai da harin, tun a shekarar 2023 Kasashen Somalia da Haddadiyar daular Larabawa suka kulla yarjejeniyar samar da tsaro.
 Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like