Wani yaro mai shekaru 10 ya rasa ransa sakamakon bude wuta da sojojin Isra’ila suka yi a zirin Gaza.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce lamarin ya faru ne a garin Han Yunus a lokacinda sojin na ısra’ila suka bude wuta a kan iyakarsu da Falasdin inda yaron mai suna Abdullah Abu Nazif ya rasu a cikin wani lambu da ya ke zaune.
Sojin Isra’ila dai na yawan kai wa Falasdinawa hare-hare a kan iyakarsu.
A gefe guda kuma ‘yan sandan ısra’ila sun kama wasu Falasdinawa 5 sakamakon zarginsu da rikici a Kudus.
Sanarwar da ‘yan sandan ta fitar ta ce, matasan sun jefi motarsu da duwatsu.
Sakamakon hakan ne aka kama su don tuhumarsu a gaban kotu.