Sojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 9


57b81c9de8b08

 

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa, ta kashe ‘yan ta’addar Boko Haram 9 tare da jikkata wasu da dama a musayar wuta da suka yi a ranar Larabar nan a garin Bulanulin da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar Kanal Sani Kukasheka Usman ya fitar da sanarwa cewa, a daren Larabar nan cewa, sun kashe ‘yan ta’addar Boko Haram a ranbar Juma’a sakamakon musayar wuta ta awa 1 da suka yi da su.

Sanarwar ta ce, sojin na Najeriya sun kuma kwato makamai, harsashai da man fetur da ma babura 9 daga hannun ‘yan ta’addar.

A daidai lokacin da hakan ta faru, sojojin Najeriya sun kama ‘yan ta’addar Boko Haram a kasuwar sayar da shanu a Maiduguri inda suke sayar da shanun da suke satowa.

Kanal Usman ya ce, ‘yan ta’addar sun yi ikirarin sato shanu 200 tare da shiga da su maiduguri ta garin Mafa.

Mutanen sun kuma ce, suna taimakawa ‘yan Boko Haram wajen sayar da shanun da suke satowa a kasuwanni.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like