Sojin Najeriya sun yi musayar wuta da ‘Yan bindiga a Bosso


 

 

Rundunar Sojin Najeriya ta ce an kashe sojojinta 11 tare da raunana wasu a wani harin kwantar bauna da ‘Yan bindiga suka kai wa sojojin a jihar Neja

Kakakin rundunar Sojin kasar Kanal Usman Kukasheka ya fadi a cikin wata sanarwa cewa akwai soja guda da ya bata, amma ya ce dakarunsu sun kashe maharan guda 8 tare da kwato makamai da dama.

Sannan Sojojin sun cafke mutane 57 bayan shafe lokaci suna musayar wuta da ‘Yan bindigar a yankin Bosso.

‘Yan bindigar sun bude wa sojojin wuta ne a yankin Bosso na Jihar Neja. Sannan babu wani cikakken bayani akan ko suwa ye ‘Yan bindigar.

You may also like