Sojin Nigeria Sun Shiga Wasu Yankunan Da Ake Rikici A Jihar Taraba


Gwamnatin tarayyar Nigeria ta tura sojoji zuwa yankunan da yan bindiga na kabilar mambila suke kisan fulani makiyaya a jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust na Najeria ta tuntubi kakakin mukaddashin shugaban kasa Laolu Akande yana cewa Osinbajo ya bada umurnin tura sojoji, yansanda da kuma jami’an yansandan ciki zuwa yankunan da ake tashe tashen hankula a jihar Taraba.

Fiye da kwanaki hudu kenan matasan kibilar mambila a karamar hukumar Sardauna suka farwa Fulani a garuruwan Toffi, Mayo Daga, Mayo Sina, Tamiya, Kwara-Kwara, Tungan Lugere, Timjire, Nguroje da wasu kauyuka da dama.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kashe mutane 90 ne zuwa yanzu sannan an sace an kashe shanu kimani 20,000.

Majiyar Daily Trust ta bayyana cewa a halin yanzu sojoji daga Yola, Serti da kuma Takum sun shiga wasu yankuna a ake rigimar kuma, lamarin ya fara lafawa.

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya nuna damuwarsa da abinda yake faruwa a karamar hukumar ta Sardauna, kuma ya yi alkawarin ganin an hukunta wadanda suke da hannu a cikin rigimar.

Sai kuma seneta mai wakiltan Taraba ta tsakiya Hon Yusuf Abubakar yusuf ya ce mutane akalla 50 aka kashe a mazabarsa kadai a cikin kwanaki hudu da suka gabata. Sannan yana zargin gwamnan jihar da rashin tabuka wani abin a zo a gani na kawo karshen rigimar.

You may also like