Shugaban rundunar Sojojin Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Lurky Irabor ya mika wa Shugaba Muhammad Buhari ainihin tutar da Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ke amfani da ita a cikin dajin Sambisa.
An mika tutar ne a wurin liyafar da rundunar tsaron fadar shugaban kasa ta shirya a Abuja.
Wannan tuta na daya daga cikin ganimar da sojojin suka samu a lokacin da suka fattattaki ‘yan Boko Haram daga dajin Sambisa. Haka kuma sun samu gano Alkur’ani da shugaban na Boko Haram ke amfani da shi wanda shi ma sun mikawa shugaban kasar.