Sojin Nijeriya: Za’a Mai Da Dajin Sambisa Wajen Horon Sojoji


4bkcf27353c0d0k44j_800c450

 

Babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya sanar da cewa za a mayar da Dajin Sambisa da ke jihar Borno a matsayin sansanin bayar da horo ga sojojin kasar bayan da sojojin suka sami nasarar kwace dajin daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram a kwanakin baya.

Rahotanni daga Nijeriyan sun bayyana cewar Janar Buratai ya bayyana hakan ne a garin Damasak na jihar Borno inda ya ce daga shekara mai kamawa ta 2017 za a mai da dajin na Sambisa wajen ba da horo ga sojoji da kuma gwajin makaman da sojojin suke da shi.

Babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Nijeriya ya ci gaba da cewa sojojin nasa suna ci gaba da tsarkake dajin na Sambisa wanda yake a matsayin babbar tungar ‘yan kungiyar ta Boko Haram yana mai cewa za su sake bude hanyar da ta hada dajin na Sambisa da gandun dajin Alagarno don kara fadada ayyukan na su, kamar yadda ya ce kuma za su kara karfafa tsaro a wajen ta yadda ‘yan Boko Haram din ba za su sake dawowa dajin ba.

A ranar Asabar din da ta gabata ce shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari ya sanar da kwace dajin na Sambisa daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram din bayan rike shi na tsawon shekaru.

You may also like