Jirgin saman sojin Nijeriya ta harba bam a sansanin ‘yan gudun hijira dake Rann a karamar hukumar Kala-Balge, jihar Borno.
Sojojin dai sun kai harin ne cikin kuskure.
Daruruwan mazauna sansanin ne suka samu raunuka inda aka tabbatar da rasuwar mutane biyu.
Jami’in Sojin Nijeriya Rabe Abubakar ya tabbatar da hakan in da ya ce lallai hakan ya faru ne cikin kuskure.
Cikin wadanda suka sami raunuka har da ma’aikatan bada agaji na MSf da ICRI.