Sojin Turkiyya sun kashe ‘yan ta’adda 13 a arewacin Iraki


 

Jiragen saman Turkiyya sun kai hari a yankunan Awashin, Basyan da Kandil na arewacin Iraki inda suka kashe ‘yan ta’adda 13.

Sanarwar da aka fitar daga helkwatar rundunar sojin ta bayyana cewa, sojin kasar sun kai hari a yankunan Awashin, Basyan da Kandil na arewacin Iraki bayan samun bayanan sirri.

An kai hari kan ‘yan ta’addar aware na PKK a Awashin da Basyan inda aka kone wasu mafakarsu guda 2 tare da kashe ‘yan ta’adda 9.

A wannan yanki na Awashin da basyan dai an sake gano wata mafakar ‘yan ta’addar inda aka yi mata ruwan bama-bamai tare da kashe ‘yan ta’adda 4.

An lalata wata mafakar ‘yan ta’addar a Kandil tare da kashe wasu mutane mambobin kungiyar a yankin.

You may also like