Sojoji da ‘yan sanda sun yi arangama a kasar Beljiyom


 

Sakamakon kara shekarun yin ritaya daga aiki da kumarage kudadaden fansho da gwamnatin Beljiyom ke ya sanya sojoji zanga-zanga inda suka fafata rikici da ‘yan sanda a Brussels babban hirnin kasar.

Gwamnatin kasar Beljiyom a wani bangare na matakan tsuke bakin aljihu na shirin kara shekarun ritayar sojoji daga 53 zuwa 63 tare da kuma rage musu kudaden fanshon da suke karba a kowanne wata.

Dubunanna sojoji ne suka halarci zanga-zangar a birnin na Brussels.

Sun ce, gwamnatin kasar ta tastar su kamar lemom tsami kuma da ma sharuddan aiyukansu nada wahala sosai.

An samu arangama da ‘yna sanda a lokacinda sojojin suka yi yunkurin haurawa fadar firaminisan kasar.

Sojojin sun dinga jifan ‘yan sandan da lemon tsami, su kuma ‘yan sanda na harba musu hayaki mai sa hawaye.

An jikkata wasu ‘yan sanda a arangamar.

You may also like