Sojoji Na Cikin Wadanda Muka Kama Suna Fashi Da Sace Mutane – Ali Kwara


Bincike ya nuna cewa mutanen da aka kama akwai sojoji a cikinsu kuma su ne suke yawancin fashi da makami da sace mutane da fasa kantuna da sayar da man fetur a kusan duka jihohin arewacin kasar nan.
Alhaji Ali Kwara shi ya yi wa ‘yan jarida bayani kan irin aikin ta’adancin da mutanen ke aiwatawa.
Yace wadanda da aka kama suna sace mutane suna kuma fashi. Kwanan nan suka sace wani dan’uwan Nuhu Ribadu mai suna Sani Ribadu, inji Ali Kwara. Kudin da suka karba hannunsa sun kai nera miliyan goma sha biyar.
A wata karamar hukuma a jihar Adamaa barayin sun kwace albashin ma’aikata da suka kai nera miliyan ishirin. Akwai wani dan majalisar jihar da suka karbi nera miliyan bakwai a hannunsa. Haka ma suka yiwa wani sirikin Atiku a Jada. A gidajen mai dake Gurore har manajan gidan mai suka kashe.
Mutanen suna fashi a hanya daga Yola zuwa Jalingo. Haka ma ta wajen Gombe zuwa Kumo suna fashi suna sace mutane. Cikin garin Gombe ma suna fashi. Gungun kungiyarsu ita ce tafi kowace kwarewa a fashi da makami a Najeriya a cewar Alhaji Ali Kwara tare da kara da cewa tunda ya fara aikinsa bai taba ganin kungiya irin tasu ba.
Akan yadda mahukuntan Najeriya ke saurin sako bata garin da shi Ali Kwara ya kama ba tare da hukumtasu ba sai yace ‘yan Najeriya sun san inda matsalar take tunda yanzu an soma dago masu shari’a. Yace tunda Najeriya take bata taba daukar hanyar gyara ba sai yanzu. Yace duk matsalar Najeriya shari’a ce. Yace duka kashe-kashen da ake yi a kasar shari’a ce babu. Rashin shari’a shi ya kawo duk fadan da ake yi, inji Alhaji Ali Kwara.
Ali Kwara ya tabbatar da sojoji na cikin wadanda aka kama. Yace Buratai ne ya kamasu da tarkon shi Ali Kwara. A irin fashin da ‘yansanda keyi Ali Kwara ya gano sojoji ne ke basu kayan aiki. Sojoji na dauko mutanensu daga jihar Yobe suna kaiwa Tivi ‘yan banga. Yace suna raba yara zuwa Niger, Kebbi, Sokoto da sauran wurare a arewa domin yin aika-aika. Ya gano duk shirinsu ya kuma dana tarko, Janar Buratai kuma ya bi sawu ya kamasu.
Wasu mutanen da aka kama sun amsa laifukansu. Wani Saji Manjo yace shi sata ya keyi. Suna fashi ne a Adamawa. Su ne suka kama Gombi. Shi ma Atiku Ibrahim wanda yace yana da gidaje a Numan da Jalingo yace suna sace mutane tare da yin fashi da makami. Su ne suka sace dan majalisa daga Kango. Bayan haka sun shiga gidan Maina Gurore sun yi barna. Su kan kuma tare hanya tsakanin Numan da Jalingo.

You may also like