Sojoji sun ceto manoma biyu a Kaduna tare da kama yan bindiga uku a Kaduna


Sojojin rundunar Operation Thunder Strike sun samu nasarar ceto wasu manoma biyu a kauyen Gadani dake gundumar Gwagwada a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Manoman dukkaninsu mata suna kan hanyarsu ne ta zuwa gona lokacin da wasu da ake zargin yan bindiga ne suka sace su.

Kwamishinan harkokin tsaro na jihar Kaduna, Samuel Aruwan shi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Bayan da sojoji suka samu nasarar ceto su, sun bu sawun yan bindigar inda suka tarfa su a kauyen Gajina suka kama uku daga ciki tare da jikkata wasu da dama.

Kwamishinan ya kara da cewa suma jami’an yan sanda sun samu nasarar ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a wajejen yankin Kurmin Idon dake kan hanyar Kaduna-Kachia a karamar hukumar Kajuru ta jihar.

You may also like