Sojoji sun kama kwamandan kungiyar Boko Haram a jihar Benue


Rundunar sojin Najeriya ta kama wani mutum mai suna Aminu Yaminu wanda ake zarginsa da kasancewa kwamandan kungiyar Boko Haram.

Ana zargin Yaminu da kitsa dukkanin hare-haren da ake kaiwa jihar Benue na baya-bayannan.

Dakarun soja na musamman da suka fito daga Birged ta 707 tare da jami’an yan sanda da kuma na hukumar tsaro ta farin kaya sune suka samu nasarar damke shi ranar Juma’a a Makurdi babban birnin jihar.

“Bayan samun wasu rahotannin sirri an gano cewa Aminu ya kammala dukkanin wasu shirye-shirye tare da mutanensa dake jihohin Nasarawa, Bauchi, Borno da kuma Yobe na kaddamar da wani gagarumin hari kan mutanen jihar Benue da basu ba su gani ba,”a cewar sanarwar da, Olabisi Ayeni,mataimakin daraktan hulda da jama’a na Birged 707 ta musamman dake Makurdi.

Jihar Benue ta dade tana fama da rikici da ake danganta shi da rikicin fulani da makiyaya.

Kama Yaminu da aka yi zai kawo canji sosai a yakin da ake na kawo karshen rikicin.

You may also like