Dakarun ‘Lafiya Dole’ sun kama likitan dake kula da mayakan Boko Haram, da kuma wasu yan kungiyar Boko Haram kimanin 963 a Maiduguri.
Shugaban Dakarun, Lucky Irabor a yau Laraba ya ce sojoji sun kuma kashe mayakan fiye 100.
Sojojin sun kuma karbi wasu mata da yara 119 da sojojin Kamaru suka kubutar a yankin Banki.
Jagoran dakarun Janar Irabor ya ce sojojin sun kuma kai jerin hare-hare ta sama a Sambisa kusan sau 68 daga ranar 8 zuwa 9 ga watan nan da muke ciki inda suka tarwatsa wata motar Hillux dauke da Bama-Bamai da mayakan suka nufi kauyen Malamfatori da ita domin kai hari.
Kazalika yace sojojin ruwa sun kwato kananan jiragen ruwa mallakin Boko Haram guda 4 a yankin tafkin Chadi.
Janar Irabor ya kuma ce sun gano makamai da Bama-Bamai da kakin sojoji da mayakan ke amfani dasu.