Dakarun sojojin Nijeriya da suke sintiri a garin Mararrabar jihar Nassarawa da Abuja sun yi nasarar kama wani dauke da makamai a yayin da suke gudanar ds aiki a shingen tsaro a jiya Alhamis.
Wanda ake zargin wanda ya bayyana sunansa a matsayin Peter Iorlaha, an kama shine da jaka wadda take dauke da bindigu, harsashai, tocila, kayan tsibbu, wayar salula kirar Tecno da sauransu.
A yayin bincike, wanda akw zargin ya bayyana cewa wani Kawunsa ne ya ba shi makaman domin ya ajiye masa. Yanzu haka dai ana ci gaba da binciken wanda ake zargin.