Sojoji Sun Kama Masu YiWa Boko Haram Safarar Miyagun Kwayoyi Da Man Fetur



A yayin farautar da Dakarun Opration Lafiya Dole suka fita daga Bama zuwa Pulka, sun yi nasarar cin karo da wasu miyagun kwayoyi da sauran kayayyaki da aka yo safararsu daga yankin Firgi da Zawan duk a karamar hukumar Bama a jihar Borno, inda wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suke kokarin shiga da kayan cikin dajin Sambisa a jiya Lahadi.

Bayan sojojin sun bi su sun yi nasarar kama daya daga cikin su mai suna Kadiri Umate mai shekaru 35, yayin da sauran suka gudu cikin daji.

Bayan magunguna da aka aka gano, sauran kayan da aka kama sun hada da gishiri, kayan sawa, takalma, maganin kashe kwari, yada, keke da sauransu.

Yanzu haka ana kan binciken wanda aka kama din.

A wani labari makamancin haka kuma, ‘yan banga sun yi nasarar kama wani mai suna Fantoma Lasani wanda yake yi wa ‘yan Boko Haram safarar man fetur a yankin Tashar Muna a yayin da ya zo daukar matasa domin barin garin Maiduguri.

Mutumin dan asalin kauyen Flatari dake karamar hukumar Bama, yana daga cikin wadanda suke yi wa ‘yan Boko Haram safarar man fetur a tsakanin yankunan Bama, Gwoza da yankin Sambisa.

You may also like