Sojoji sun kama mutane 9 kan kisan dan majalisar dokokin jihar Taraba


Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama mutane 9 da ake zargi da hannu a yin garkuwa da kuma kisan ɗan majalisar dokokin jihar Taraba, Hosea Ibi.

Ibi dake wakiltar mazabar Takum II a majalisar dokokin jihar wasu yan bindiga ne suka yi garkuwa da shi a garin Takum lokacin da ake tsaka da bukukuwan shiga sabuwar shekarar 2018.

Sojojin Birged ta 23 da aka tura Jalingo a karkashin atisayen “Gudun Mage” da kuma wata tawagar jami’an hukumar tsaro ta farin kaya DSS daga Jalingo sun gudanar da bincike a cikin garin Takum a ranar Asabar 24 ga watan Faburairu, inda suka kama mutanen.

Mutanen da aka kama sun haɗa da Jaka Ejukun (shekaru 24), Peter Isaga (shekaru 33) da Arachukwu Bedforth (shekara 21).

Sojojin sun gudanar da wani binciken inda  suka kama karin wasu mutane  a yankin Gbise dake karamar hukumar Katsina Ala ta jihar Benue.

Wadanda aka kama a Katsina Ala sun hada da Isaiah Suwe (shekaru 23) dan kabilar Tiv daga karamar hukumar Lessel Ushongo ta jihar Benue, Amadu Barnarbas Torva (da aka fi sani da  Atamanin) (shekaru 23 ) daga Gbise karamar hukumar Katsina Ala,Benue , Aondi Teroo (shekaru 21), Nengenen Mbaawuaga Damian (shekaru 22), Aondoase Kayitor (shekaru 18 ) da kums Ternenge Tersoo (shekaru 19 ).

Jumullar mutane 9 aka kama kan zargin garkuwa da kuma kisan Hosea Ibi.

You may also like