Sojoji sun kama mutane shida dake karkatar da akalar mai zuwa kasuwar bayan fage a Kaduna


Hoton sojin Najeriya

Sojoji sun kama mutane 6 da ake zargi da karkatarwa da kuma sayar da man fetur ta hanyar yin amfani da motar tanka mallakin kamfanin NNPC a garin Zonkwa dake Karamar Hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.

Kwamandan rundunar samar da tsaro a yankin, Kanal Idong Ekpeyong,ya fadawa manema labarai a garin Kafanchan cewa an kama mutanen da ake zargi lokacin da tankar ke juye man a gidan man Lesar dake kan hanyar Kachia a Zonkwa.

Ekpeyong ya ce man an turo shine daga Lagos zuwa gidan man Sambo dake Deidei a Abuja.

Mutanen da aka kama sun haɗa da Aminu Suleiman(direban motar); Ayo Marcus (mai zuba mai);  Elisha Kyauta (mai rakiyar motar);Mathew Sabo(Manajan gidan man); Yashim Daudu (Maikula da gidan man) da kuma Yusuf Yahaya wanda shine ya mallaki man fetur ɗin da aka karkatar.

Ya kuma ce za a mika mutanen ga hukumomin da suka dace domin su fuskanci hukunci.

You may also like