Sojojin Najeriya da suka fito daga Bataliya ta 93 dake Takum, jihar Taraba sun kama wani mutum da ake zarginsa da yi wa batagari leken asiri, lokacin da yake kokarin gano wani mutum da wasu batagari ke shirin kashewa.
Daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Texas Chukwu, a wata sanarwa da ya fitar jiya ya ce sojojin sun kama mutumin lokacin da suke aiwatar da shirin samar tsaro da ake kira Ayem Akpatuma.
Ya ce wani fasinja ne da suke cikin mota ya jiwo mutumin yana magana da wani, Malam Musa Ibrahim kan lalubo mutumin da za a kashe, lokacin da suke tafiya akan hanyar Takum zuwa Chanchangi.
Chukwu ya ce an sanarwa da sojoji bayanin inda suka bi motar cikin sirri suka kama shi.
Ya yin da ake masa tambayoyi mutumin ya amince da cewa yana samar da bayanai ga bata gari dake gudanar muggan aiyukansu a jihar.