Sojoji Sun kama wasu ‘Yan BokoHaram a kasuwar Shanu a garin Maiduguri. 


A safiyar jiya Laraba ne dakarun Opration Lafiya Dole tare da taimakon ‘yan banga suka kama wasu mutane uku a kasuwar shanu dake Maiduguri wadanda ake zargin membobin Boko Haram ne.
Wadanda ake zargin sun hada da Abba Go Dallagio, Abba Fanned da Alhaji Nwariye. 
A yayin da ake gudanar da bincike a kansu, sun yi ikrarin cewa sun shigo kasuwar ne ta yankin Mafa da shanu guda 200 domin su sayar.
Sun kuma kara da cewa suna daga cikin masu taimakawa Boko Haram wajen sayar musu da shanu.
A wani labari makamancin haka ma, sojojin sun kama wani jakada kuma dan leken asirin ‘yan Boko Haram mai suna Alhaji Ajid Umar a kasuwar shanun. An gano shanu kimanin 170 ta hannunsa. 
Yanzu haka ana kan ci gaba da gudanar da bincike a kansu.

You may also like