Sojojin Najeriya sun kashe ƴaƴan ƙungiyar Boko Haram 7 a wani samame da suka kai a dajin Sambisa tare da taimakon jiragen yaƙi.
Sani Usman, darakatan hulɗa da jama’a na rundunar yace sojojin sun kuma lalata motocin Hilux guda 12 da kuma wasu manyan motoci masu ɗauke da bindiga guda 11.
Usman ya ce sauran kayayyakin ƴan ta’addar da aka lalata sun haɗa da wani matsuguni dake wurin da ake kira Sansanin Zairo, bama-bamai da kuma sauran abubuwa.
Ƙari kan haka kuma jaruman sojojin sun gano bindigar kakkabo jiragen sama da harsashinta da kuma bindigar gargajiya guda ɗaya.
Usman ya ƙara da cewa sauran abubuwan da aka lalata sun haɗa da kekunan hawa 30 da kuma injin samar da wutar lantarki.
“Abin takaici sojoji biyu sun jikkata yayin kai samamen.
“Sojojin da suka jikkata tuni rundunar sojin saman Najeriya ta ɗauke su zuwa asibiti kuma suna nan suna murmurewa.”
Usman ya shawarci mazauna jihohin Adamawa, Borno da Yobe kan su kai rahoton duk wani dan Boko Haram da suka gani a yan kunansu.