Sojojin Najeriya dake aikin Atisayen AYEM AKPATUMA ya yin da suke gudanar da sintiri akan titin Dogon Dawa -Damari a jihar Kaduna sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin bata gari ne tare da gano bindigogi kirar Ak-47 guda biyu.
Sojojin sun kuma gano gidan harsashi guda uku da kuma harsashi 88 daga bata garin.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Texas Chuku, ya bayyana cewa a wani bangaren sojoji da aka ajiye akan titi Rigasa zuwa filin jirgi sun fuskanci harin kwanton bauna daga wasu mutane da ba a san ko su waye ba.
Ya kara da cewa sojoji biyu sun jikkata a harin kuma a yanzu haka suna karbar magani a asibiti.