Sojoji sun kashe yan bindiga 68 a jihar Zamfara


Rundunar sojin Najeriya, ta kashe barayi 68, tare da kama wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne su shida da kuma gano baburan hawa 17 a jihar Zamfara daga ranar 17 ga watan Afirilu ya zuwa yanzu.

Udeagbala Kennedy, kwamandan rundunar sojan Najeriya,birged ta ɗaya dake Sokoto ya bayyana haka yayin da yake mikawa kwamishinan yan sanda wadanda aka kama da laifin garkuwa da mutane su 6,a Gusau babban birnin jihar ranar Talata.

“Rundunar sojan Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun fara atisayen kakkabe duk kanin barayi da kuma kawo karshen aikata ayyukan sata da kashe-kashe a jihar.”ya ce.

“Yau sojoji da kuma sauran hukumomin tsaro sun samu nasarar gudanar da kai farmaki a kowane lungu da sako dake jihar hakan ne ya kawo nasarar da aka samu.”

Ya kara da cewa a tsawon lokacin an samu nasarar kashe yan bindiga 68 amma kuma abin takaici sun rasa sojoji biyu.

You may also like