Sojoji Sun Kashe Yan Kungiyar Boko Haram 13Sojojin da suke aiki karkashin shirin samar da tsaro a yankin arewa maso gabas da ake kira Operation Lafiya Dole, sun kashe yan kungiyar Boko Haram a sama da 13 a  yankuna daban-daban  na jihohin Adamawa da Borno.

 Mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Janar Sani Usman,ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar  inda yace an kashe yan kungiyar 12 a wani harin kwanton bauna da sojoji suka kai musu a mahadar hanyar Miyanti-Banki dake Borno da kuma Kafin Hausa a Madagali dake jihar Adamawa. 

Usman yakara da cewa an kashe wasu yan kungiyar da dama a kan hanyar Dukje-Mada  kusa da kauyen Gulumba gana.

” Amma abin takaici sojoji biyu sun rasa rayukansu lokacin da motar da suke ciki ta taka nakiya da aka binne akan hanya,yayin da guda hudu suka samu raunuka. 

“An an dawo  da gawarwakin jajirtattum sojojin da suka mutu  da kuma wadanda suka jikkata birnin Maiduguri, ” Usman yace.

Ya lissafa kayayyakin da aka kwato daga hannun yan ta’addar da suka hada da keken hawa 18, buhun fulawa 30,buhun gyada daya, buhun gishiri,bandir din yadi, huhun goro guda biyu, tocilan da kuma sauran kayayyaki.

 

You may also like