Sojojin Najeriya dake aiki a karkashin shirin samar da tsaro a yankin arewa maso gabas da akewa kira Operation Lafiya Dole sun samu nasarar ceto fararen hula 2000 suka kuma kashe mayakan ƙungiyar Boko Haram da dama a wani samame da suka kai wasu tsibirai dake cikin tafkin Caji.
Kwamandan rundunar ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas shine ya bayyana haka yayin wani jawabi da yayiwa manema labarai a hedikwatar dake kula da yaƙin da ake a yankin arewa maso dake Maiduguri.
Ya kara da cewa sojojin sun kuma samu nasarar ceto daya daga cikin yan matan Chibok da aka sace.
Binciken farko ya nuna cewa ƙaramar yarinyar da aka gano mai suna Salomu Pagu tayi daidai da yarinyar dake da namba ta 86 a jerin sunayen yan matan Chibok da aka buga.
Yarinyar na tare da rakiyar wata karamar yarinya Jamila Adams mai shekaru 14 wacce ke dauke da yaro dukkaninsu na samun kulawa daga rundunar soja.