Sojoji sun sake kwato garin Boni na kasar Mali


A ranar Juma’a da rana ne mayaka masu da’awar jihadi suka karbe ikon garin na Boni har ya zuwa sanyin safiyar ranar Asabar kafin sojoji su fatattake su.

 

Sojojin Mali sun kwato garin Boni da ke tsakiyar kasar bayan karbe ikon garin da mayaka masu ikirarin jihadi suka yi na dan wani lokaci. Sojojin Mali da na Majalisar Dinkin Duniya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kungiyar mayakan jihadin wadda ba a bayyana sunanta ba, sun yi awon gaba da wani jami’i na gundumar yankin wanda suka yi garkuwa da shi.

A ranar Juma’a da rana ne mayakan masu da’awar jihadi suka karbe ikon garin na Boni har ya zuwa sanyin safiyar wannan Asabar din kafin sojoji su fatattake su. Wata majiya mai kusanci da rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali wadda ake yi wa lakabi da MINUSMA ta ce a yanzu haka wasu jirage biyu masu saukar ungulu suna shawagi a sama domin karfafa wa sojojin Malin wadanda ke iko da garin a yanzu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like