Sojoji za su kubutar da yan matan Dapchi cikin mako daya ko biyu – Dan-Ali



Yan mata 110 na makarantar sakandaren Dapchi da yan kungiyar Boko Haram suka sace za su samu yancin su nan ba da dadewa ya yin da sojoji suke kusa cim ma su.

Ministan tsaro Mansur Dan-Ali shine ya bada wannan tabbacin ya yin da ake tattaunawa da shi a ranar Asabar a wata tattaunawa da gidan Talabijin Na Channels.

“Zai iya kasancewa da wuri; watakila sati guda, zai iya kasancewa sati biyu, amma muna aiki a kan batun,  ina fada maka  da gaskiya cewa gab muke da cim ma su,” ya fadawa gidan Talabijin.

Yan ta’addar sun mamaye makarantar yan matan dake Dapchi a ranar 19 ga watan Faburairu inda su ka yi awon gaba da yan matan.

Ministan ya bayyana cewa ana kan yin dukkanin wani kokari na tabbatar da cewa an kubutar da yan matan lami lafiya cikin kankanin lokaci.

Dan-Ali ya bayyana kwarin gwiwarsa, lallai yan matan za su dawo gidajensu cikin kankanin lokaci  ta yin la’akari da bayanan sirri da gwamnati take dasu. 

You may also like