Kakakin Sojin Sudan ta Kudu ya sanar da kai hari kan Dakarun ‘yan tawaye a arewacin kasar.
Kakakin Dakarun Sudan ta Kudu Mista Santo Dominiv Chul ya sanar a wannan Alkhamis cewa Sojojin kasar sun kai hari a wuraren Dakarun ‘yan tawaye kusa da garin Malakal dake arewacin kasar a Jiya Laraba.saidai Mista Santo Dominiv Chul bai yi wani garin haske ba dangane da yadda gumurzun ya kasance a yayin kai harin.
Garin Malakal na daga cikin manya- manyan buranan kasar Sudan ta kudu da suka kasance filin daga tsakanin mayakan ‘yan tawaye da Dakarun Gwamnati tun bayan da kasar ta fada cikin yakin basasa a watan Decembar na shekarar 2013.