Sojojin Gwamnatin Iraki Suna Ci Gaba Da Murkushe ‘Yan Ta’addan Da’ish A Garin Mosel


 

 

Majiyar rundunar sojin Iraki ta sanar da halakar ‘yan kungiyar ta’addanci ta Da’ish da dama a farmakin da jami’an tsaron kasar suka fara kaddamarwa da nufin ‘yantar da garin Mosel daga mamayar ‘yan ta’addan.

Jiragen saman yakin sojin Iraki sun kai farmaki kan sansanoni da wajajen buyan ‘yan ta’addan kungiyar Da’ish a yankuna da dama da suke garin na Mosel a safiyar yau Litinin, inda suka kashe ‘yan ta’adda masu yawa.

Rahotonni sun bayyana cewa: Jiragen saman yakin na rundunar sojin Iraki sun tarwatsa sansanoni biyar na ‘yan ta’addan Da’ish a garin Sharqat tare da kai hare-hare kan duk wani motsin da ‘yan ta’addan zasu yi da nufin canja matsuguni.

Gidan talabijin na Almayadeen ya habarta cewa: Sojojin gwamnatin Iraki sun ‘yantar da kauyuka da dama daga mamayar ‘yan ta’adda da suke kudu maso gabashin garin na Mosel, Kamar yadda suka kwace iko da sansanin Namroud da ke gabashin garin na Mosel a yau Litinin.

A kudancin garin Mosel kuwa ‘yan kunan bakin waken kungiyar Da’ish hudu ne suka sheka lahira a lokacin da suke kokarin kai hari kan wajajen binciken sojin Iraki a yau Litinin.

Yantar da garin Mosel dai yana matsayin kawo karshen daular Musulunci ta ‘yan ta’adda da kungiyar Da’ish ta kafa a kasar Iraki a cikin watan Yunin shekara ta 2014 karkashin khalifancin Abubakar Al-Baghdadi.

You may also like