Sojojin Hadin Gwiwa Na Najeriya Da Kamaru Sun Yi Nasarar Kashe Wasu ‘Yan Boko Haram. 



Sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar na Kamaru sun yi wani gagarumin nasara akan yan ta’addan Boko Haram a hanyar iyakar da ta sada kasashen guda biyu.
Majiyarmu  ta ruwaito cewa an gano  ‘yan ta’addan da suka tsere daga dajin Sambisa na buya ne a yankunan dake kan iyakokin kasashen.
Kanal Dourai da Laftanal Kanal Mohaman na hukumar tsaron Kamaru ne suka jagoranci tawagar tare da taimakon bataliya ta 151 ta hukumar sojin Nijeriya.
Dakarun sojojin sun kakkabe yan ta’adan a yankunan Siyara, Kote, Sigawa,  kafin su yunkura zuwa kauyukan Bulabundibe, Adeleke, Tchatike da kuma Lamukura.
A yayin artabun ‘yan ta’adda da dama sun mutu yayin da aka damke  wasu daga cikin su. Wasu  sun tsere da raunuka sakamakon harbin bindiga.
Abubuwan da aka samu bayan arangamar sun hada da mota kirar Toyota kanta, bindigogi biyar,  tutar ‘yan ta’addan guda biyar, tayoyin mota guda hudu da kuma babura guda biyu.
Kanal Dourai yace aikin ya kasance wata nasara gurin inganta tsaro a iyakar, sannan kuma ya yabawa hukumar sojin Najeriya kan rawar da suka taka.

You may also like