Dakarun Iraki sun samu nasarar kwace iko da garin Al-Qayyarah daga hannun kungiyar IS. Garin na Al-Qayyarah dai na kusa da birnin Mosul da ‘yan kungiyar ta IS suke da karfi.Dakarun Iraki sun samu narar kwace garin Al-Qayyarah
Kwamandan dakarun na Iraki da ke samun goyon bayan sojojin Amirka a yankin da suke da IS din, Nejm al-Jabouri ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewa tuni ma sojojinsa suka kwace iko da matatar mai da ke garin. Sai dai al-Jabouri ya nunar da cewa wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da kungiyra ta IS takai da motoci ya dakile yunkurin da dakarunsa ke yi na sake kutsawa wasu yankunan garin na Al-Qayyarah da ke da nisan kilomita 60 da kudancin birnin na Mosul.