Sojojin Kawancen Amurka Sun Kai Hari Kan Sansanin Dakarun Sa Kai Na Iraki


 

 

Rundunar sojin sa kai na al’ummar kasar Iraki ta sanar da cewa, a daren jiya sojin kawancen Amurka da ke da’awar yaki da kungiyar ISIS a Iraki, sun harba makamai mai linzami a kan sansanin sojin sa kan a Tala’afar da ke kusa da Mosul.

Bayanin ya ce wannan harin ya zo ne jim kadan bayan kammala wani zama tsakanin Firayi ministan kasar Iraki haidar Abadi da kuma kuma wasu manyan kwamandojojin rundunar sojin sa kan ta al’ummar Iraki.

Bayanin ya ce wasu daga cikin manyan kwamandojin sojin sa kan na Iraki sun samu raunuka, a kan rundunar sojin sa kan Iraki ta bukaci kawancen Amurka da ya yi bayani kan wannan hari da aka kai, wanda aka yi amfani da makami mai linzami da ake saitawa da hasken laser wajen kai harin, kuma hakan ya faru a daidai lokacin da wani jirgin sojojin kawancen ke shawagi ne a wurin.

You may also like