Sojojin Najeriya Sun kama yan Ta’addar Niger delta.


 

 

Sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu mutum biyu da ake zargin yan Kungiyar Niger Delta Avengers ne a daf da barikin sojonin ruwa na garin warri.  

Wadanda aka kama din ana kyautata zaton suna da Hannu a Harin da aka kaiwa kamfanin hako man fetur na CHEVRON NIGERIA LIMITED a watannin Mayu da julin da suka gabata na wannan shekarar.

Mutane biyun masu suna  Stanley Toghan da Felix Miyenminiye a garin Sapele dake warri na jihar Delta.

A gefe guda kuma Shugaban yan asalin biafra(IPOB)  wato Nnmadi Kanu ya musanta zargin da ake masa na cewar yana da hannu akan ayyukan yan ta’addan.  

Kungiyoyin dai guda biyu wato MEND- movement for the emancipation of niger delta da kuma NDA- Niger delta sun dade sunayi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta hanya fasa bututun danyen man fetur da suke yi.

You may also like