Sojojin Najeriya Sun Kashe Abu Nazir Kwamandan Boko Haram Sun Kuma Ceto Yara 9Rundunar sojin Najeriya tace ta kakkabe yan ta’adda  a kauyen jarawa dake karamar hukumar Kala Balge ta jihar Borno, bayan da ta sami bayanan sirri dake nuni da cewa yan kungiyar Boko Haram na tattaruwa a yankin. 

Sojojin bataliya ta 3 ,dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Lafiya Dole, da hadin gwiwar yan kungiyar samar da tsaro ta sakai da aka fi sani da Civilian JTF suka kai farmakin kan yan kungiyar. 

 Kimanin kilomita daya daga kauyen Jarawa sojojin sun fuskanci harin kwanton bauna daga yan kungiyar Boko Haram amma sunyi nasarar dakile harin   bayan an dau lokaci ana musayar wuta. A cewar mai magana da yawun rundunar Sojin, Sani Usman. 

Usman ya cigaba da cewa sojojin sun samu nasarar kashe yan ta’addar masu yawan gaske,ciki har da wani fitaccen dan kungiyar wanda shine Amir na yankin Jarawa mai suna Abu Nazir.

Haka kuma Sojojin sun samu nasarar kwato makamai da dama ciki har da bindiga kirar AK-47.

Har ila yau rundunar ta samu nasarar ceto wasu yara su 9 da kungiyar ta Boko Haram ke bawa horo a sansaninsu na bada horo dake kauyen. 

Tuni aka debe yaran daga sansanin ana kuma gudanar da bincike kafin daga bisani a mika su ga kwamitin kula da sansanin yan gudun hijira na garin Kala Balge.  

You may also like