Rundunar sojin Najeriya a ranar Juma’a ta kashe wasu yan bindiga goma lokacin da take gudanar da wani atisaye na kakkabe maharan dake yankin Numan a jihar Adamawa.
A wata sanarwa mai dauke da sahannun, Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Texas Chukwu, ta ce yan bindigar su goma an kashe sune yayin wani farmaki da rundunar ta kai da ya dauki tsawon sa’a guda.
Ya bayyana cewa daya daga cikin yan bindigar mai suna,Adamu Umar an kama shi da ransa kuma tuni aka mika shi ga jami’an tsaro domin su cigaba da bincike.
Birgediya Janar, Texas Chukwu ya kara da cewa, sojojin sun kuma samu nasarar samun baburan hawa goma, bindigogi kirar gida guda biyu, harsashi , wasu bindigogi guda biyu da kuma adda.