Rundunar sojin Najeriya a ranar Litinin ta ce dakarunta sun samu nasarar lalata wani sansanin bada horo na kungiyar Boko Haram dake Benisheikh a jihar Borno.
Kanal Onyeama Nwachuku, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri.
Nwachuku, ya ce sojojin sun kuma kashe dan kungiyar daya tare da ceto wani mutum guda da yan ta’addar ke tsare da shi a maboyarsu dake Afa, a ranar Lahadi.
Ya ce sojojin sun dogara ga bayanan sirrin da suka samu wajen gano sansanin da ake bawa mayakan kungiyar horo.
Ya yin samamen da suka kai sansanin sojojin sun yi a rangama da yayan ƙungiyar da suke barin sansanin cikin gaggawa.