Rahotanni daga yankin Kareto dake jihar Borno sun tabbatar da kame wasu masu yi wa ‘yan Boko Haram leken asiri.
Kakakin rundunar sojojin Nijeriya Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka shi ya bayyana ga manema labarai haka, inda ya kara da cewa an gano mutanen ne a wani bincike da rundunar ta gudanar, wadanda suka bayyana cewa suna kewayawa ne tare da fakon idanun mutane.
Sun kuma kara da cewa yawancin hare haren da ake kai wa arewacin Borno da hadin bakin su a ciki.
A ‘yan makonnin nan dai rundunar ta zafafa bincike a dukkannin kusurwoyin jihar Borno, tare kira ga gwamnatin tarayya ta amince da samar musu da barikin sojoji cikin dajin Sambisa, saboda hana duk wasu batagari samun mafaka a cikin dajin.
Har wa yau kuma rundunar tana neman gwamnati ta gyara titunan Lamar tare da zuba kwalta wanda zai kama daga Damboa zuwa garin Yola. Rundunar ta ce zuba da kwalta adajin Sambisa ba karamin dadin hakan za su ji ba.
A yayin samamen da rundunar sojin ra gudanar ta gano makamai da motocin yaki da dama wadanda aka samu daga hannun kungiyar Boko Haram.