Sojojin Najeriya sunyi karyar Raunata ni – Abubakar Shekau


Kungiyar Boko Haram bangaren Abubakar Shekau ta fitar da wani sabon faifan bidiyo, a inda Shekau din ya karyata sojojin Najeriya cewa sun raunata shi.
A cikin faifan bidiyon wanda kungiyar ta fitar da sanyin safiyar ranar Lahadi, Abubakar Shekau ya kwashe kimanin minti 30 yana magana da harsunan Hausa da Larabaci da kuma Kanuri.

Da fari dai ya karyata rundunar sojin Najeriya da ta bayar da sanarwar rauna shi a wani harin sama da ta ce ta kai kan ‘yan Boko Haram.

Shekau ya ce yana nan lafiya kalau babu abin da ya same shi.

Baya ga karyata sojojin, Abubakar Shekau ya bayyana Najeriya da kasar kafirci, a inda ya rera taken Najeriya da Turanci, bayan ya bayyana shi da wata alama ta kafirci.

Ya kuma sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a Najeriya, har zuwa lokacin da kasar za ta koma kan tafarki irin nasu.

Har wa yau, Shekau ya ja hankalin mabiya mazhabar Shi’a a Najeriya da kuma jagoransu, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da cewa su tuba domin abin da suke yi ba musulunci ba ne.

Ya kuma kara da cewa bin tafarkin da ‘yan Boko Haram suke bi ne kawai mafita ga mabiya mazhabar ta Shi’a.

Sharhi

Sojojin Najeriya sun sha ikrarin kashe Abubakar Shekau, a yayin wasu hare-haren da suke kai wa Dajin Sabisa.

Kuma a duk lokacin da suka yi irin wannan ikrarin, Shekau din da kansa yake fitowa ya karyata batun nasu.

Ikrarin sojojin kan illata Shekau na baya-bayan nan shi ne wanda sojojin kasar suka ce wani hari da dakarun sama suka kai ya kashe wasu jiga-jigai a ƙungiyar Boko Haram.

A wata sanarwa da kakakin sojan ƙasa, Kanar Sani Kukasheka Usman ya fitar ta ce, an jikkata daya daga cikin shugabannin Boko Haram, wato Abubakar Shekau.

Daga cikin manyan ‘yan kungiyar ta Boko Haram da aka kashe yayin harin sun haɗa da Abubakar Mubi, da Malam Nuhu da Malam Hamman.

Sanarwar ta kuma ce, an kai harin ne a ƙauyen Taye dake yankin Gombale, dake dajin Sambisa.

Boko Haram da Shi’a

Kungiyar ta Boko Haram dai, a faya-fayan bidiyon da ta dade tana fitarwa, ta sha sukar mabiya mazhabar Shi’a.

Ta kuma sha alwashin kaddamar da hare-hare a kan mabiya mazhabar, baya ga kiran jagoran kungiyar ta Shi’a, El-zakzaky da ya tuba.

A shekarar da ta gabata ne kuma aka kai wa ‘yan Shi’ar harin kunar-bakin-wake a yayin wani tattaki da suke yi zuwa birnin Zaria.

Jim kadan bayan faruwar al’amarin, kungiyar ta Boko Haram ta dauki alhakin kai harin a kan ‘yan Shi’a, a inda ta bayyana su da wadanda ba musulmai ba.

Boko Haram dai tana ikrarin ginuwa a kan akidun Ahlussunnah da sahabbai suka bi, a inda su kuma ‘yan Shi’a suke cewa suna bin mazhabar Iyalan gidan annabi ne.

Ko a kasashe kamar Iraq da Syria da Yemen da ma Saudiyya, ana samun yanayin da kungiyar IS wadda Boko Haram ta yi wa Mubaya’a, ke halasta jinin ‘yan Shi’a.

Boko Haram ta dare gida biyu

Yanzu haka za a iya cewa kan ‘yan kungiyar Boko Haram ya rabu gida biyu, tsakanin tsagin Abubakar Shekau da na Albarnawi wanda aka ce dan tsohon shugaban kungiyr ne, Muhammad Yusuf.

Ana zaton cewa rarrabuwar kan dai ta samo asali ne daga kallon da bangaren Albarnawi suke yi wa bangaren Shekau da zarmewa wajen zafafa hare-hare a kan mutanen da ba su ji ba su gani ba.

Yanzu haka dai Albarnawi ne shugaban kungiyar ta Boko Haram da kungiyar IS ta san da zamansa a Najeriya.

You may also like