Rundunar sojan Nigeria ta ce wasu dakarun ta sun ɓace a jihar Borno, bayan da ‘yan Boko Haram suka yi musu kwanton ɓauna a ƙauyen Guro Gongon.
Kakakin rundunar sojan Kanal Sani Usman Kuka-Sheka ya sheda wa BBC ce wa dakarun na su suna kan hanyar komawa sansanin su ne, bayan sun je farautar yan Boko Haram, inda suka kuma samu gagarumar nasara.
Kuka-Sheka yace sojojin sun kashe ‘yan Boko Haram da dama, sun kuma kwato manyan makamai da kanana, da kayan abinci, gami kuma da lalata maɓoyar ‘yan Boko Haram din.
Jami’in ya ce a kan hanyar dakarun na su ne ta koma wa, wasu ‘yan Boko Haram suka yi wa sojojin kwanton ɓauna, inda aka yi mummunar musayar wuta, aka kashe ‘yan Boko Haram da dama, yayin da a ɓangaren sojoji kuma aka jiwa 19 rauni, sannan aka kuma ji wa wasu civilin JTF su uku da ke yi wa sojoji rakiya rauni.
Kanal Kuka-Sheka yace a nan ne kuma da dama daga dakarun na su suka ɓace, to sai dai yace daga baya wasu sun fara komawa sansanin na su.
Kakakin ya ce an tura wasu sojojin ƙundumbala domin nemo sojojin da suka ɓace.
Sai dai bai bayyana cewa ko ‘yan Boko Haram ne suka kama sojojin ba, kuma bai bayyana adadin sojojin da suka ɓace ba, sannan bai bayyana cewa ko an kashe wasu daga cikin su ba.