SOJOJIN NIGERIA SUN SUN SALLAMI AHMED BOLORI


Rundunar sojin Najeriya ta sallami, Ahmed Bolori bayan ta yi masa wasu tambayoyi.
Ahmed Bolori dai na daya daga cikin mutum uku da rundunar ta ba da sanarwar cewa tana nemansu ruwa-a-jallo.

Hakan ya faru ne bayan wani hoton bidiyo dauke da ‘yan matan Chibok da kungiyar boko haram ta fitar, kasancewar sai da suka samu bidiyon kafin kungiyar ta sanya shi a intanet.

Ahmed Bolori ya shaida wa’ yan jaridu cewa sojojin sun ce kuskure ne suka yi wajen bayyana cewa suna nemansa ruwa a jallo ba, alhalin suna son ya je ne ya taimaka dana samu shawo kan matsalar da ake fuskanta ta Boko Haram.

Bolori ya kara da cewa ce babu wani batanci da sojojin suka yi masa, kuma sun tattauna kan batutuwan tsaro da sauran su, kuma sun sake shi ne bisa sharadin duk lokacin da suka bukace shi zai gabatar da kansa.Sai dai ya ce bai san inda ‘yan Boko Haram su ke ba ko kuma ‘yan matan Chibok suke ba.

You may also like