Sojojin Nijeriya Sun Dawo Daga Dajin Sambisa Tare da Mata da Yara 605


 

Sojojin Nijeriya sun dawo daga dajin Sambisa inda suka yi nasarar ceto mata da yara har guda 605.

Kwamandan rundunar Leo Irabor shi ya bayyana haka a wani taron manema labarai a hedikwatar rundunar ta Lafiya Dole a Maiduguri.

Irabor ya kuma ce rudunar na ci gaba a samun nasarori a yakin da take da ta’addanci a dajin Sambisa.

Ya ce, a lokacin da ake gudanar da ofireshon din ne aka ceto maza guda 69, mata 180, yara maza guda 227 da yara mata guda 126 tsakanin 7 ga watan Disamba da 14 ga watan Disambar nan.

Ya ce wadanda aka ceto din suna hannun su, kuma za su yi musu tambaoyi su kuma gudanar da bincike akan su.

 

Ya kara da cewa, rundunarsa a shirye ta ke ta share sauran kamu kamun ‘yan ta’addan daga maboyar su, kuma izuwa yanzu sun samu ci gaba a kan hakan.

army-sambisa

You may also like