Sojojin Nijeriya Sun Kama ‘Yan Boko Haram 1400 Cikin Kwanaki 8 Da Suka Gabata


 

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da cewa cikin kwanaki takwas din da suka gabata, sojojin Nijeriyan sun sami nasarar kame kimanin mutane 1,400 da ake zargi ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram ne.

Kwamandan da ke  jagorantar hare-haren sojin nan na “Operation Lafiya Dole” da ake gudanarwa da nufin kawo karshen ‘yan ta’addan Boko Haram Manjo Janar Lucky Irabor ne ya bayyana hakan a ganawa da manema labarai na mako mako da ya saba yi don karin bayani kan ayyukan da sojojin nasa suke yi a jihohi shida na arewa maso gabashin Nijeriyan inda ya ce cikin kwanakin takwas din da suka gabata sojojin nasa sun sami nasarar kame kimanin mutane 1400 da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram din ne.

Janar Irabor ya kara da cewa tun dai bayan da sojojin suka sami nasarar kwace dajin Sambisa daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram din, ya zuwa yanzu sun sami nasarar tsarkake wasu kauyuka da dama na jihohin Borno da Yoben daga gyauron ‘yan Boko Haram din.

Adadin mutanen da sojojin suka kama tun bayan kwace dajin Sambisan dai ya kai mutane 2700 kenan bayan wadanda Janar Irabon ya ce sun kama wasu a dajin na Sambisa da kewaye da ya ce adadinsu ya kai mutane 1240.

A karshen shekarar da ta gabata ta 2016 ne dai shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari ya sanar da nasarar da sojojin suka samu na kwace dajin Sambisan wanda yake a matsayar helkwatar ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

You may also like