Sojojin Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Boko Haram Da Dama A Wani Gumurzu


Rahotanni daga jihar Borno sun bayyana cewar sojojin Nijeriya sun sami nasarar hallaka ‘yan kungiyar Boko Haram da dama tare da raunata wasu da dama a wani gumurzu da ya gudana tsakanin bangarorin biyun.

Majiyarmu ta PREMIUM TIMES ta bayyana cewa wata majiya ta shaida mata cewa musayar wutan ya faru ne a lokacin da ‘yan Boko Haram din suka kai hari kan wata bataliyan sojoji ta 119 da ke Kangarwa inda sojojin Nijeriyan suka mayar musu da martani, inda suka yi nasara halaka ‘yan bindigan tare da raunata wasu.

Majiyar ta kara da cewa wasu sojoji guda 9 sun sami raunuka yayin gumurzun sai dai babu wani da ya rasa ransa.
Wannan dai ba shi karon farko da dakarun Nijeriya suke fuskantar irin wadannan hare-hare daga wajen ‘yan Boko Haram din ba. Wasu majiyoyi sun ce wannan shi ne karo na shida da wannan bataliya take fuskantar irin wadannan hare-hare na ba za ta daga Boko Haram din.

You may also like