Sojojin Nijeriya Sun Kwace Tungar Boko Haram Na Karshe A Dajin Sambisa


 

 

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya sanar da cewa sojojin kasar sun sami nasarar fatattakar ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram daga babbar maboyarsu a dajin Sambisa wadda ke a matsayin wata alama ta kawo karshen ‘yan ta’addan.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a yau din nan Asabar inda ya ce babban hafsan hafsoshin sojin kasar Tukur Buratai ya shaida masa cewa sojojin sun kwace babbar tungar ‘yan Boko Haram din a Dajin na Sambisa ne a jiya Juma’a lamarin da ya ce labari ne mai faranta rai wanda ya jima yana jiran jinsa.

Shugaba Buhari ya ce zai yi amfani da wannan damar wajen “jinjina wa sojojin Nijeriyan na “Operation Lafiya Dole” saboda irin wannan gagarumin jaruntakar da suka nuna na kwace wannan tungar da aka kira da ‘Camp Zero’ wanda ke tsakiyar dajin na Sambisa, kamar yadda kuma ya kirayi ‘yan Nijeriyan da su ci gaba da ba da hadin kai ga sojojin kasar wajen ba su labarai a kokarin da suke yi na kawo karshen Boko Haram din a kasar baki daya.

A ‘yan makonnin da suka gabata dai  sojojin Nijeriyan suka kaddamar da wasu manyan hare-hare a dajin Sambisan dake jihar Borno da nufin fatattakan ‘yan Boko Haram daga wajen.

Rahotanni dai ‘yan Boko Haram din sun halaka sama da mutane dubu 15 da kuma tarwatsa wasu mutanen da suka dara  miliyan biyu daga muhallansu tsawon shekaru 7 da suka yi suna gudanar da wadannan ayyuka na su na ta’addanci musamman a jihoji Arewa Maso Gabashin Nijeriyan.

You may also like