Sojojin Nijeriya Sun Kwato Mutane 85 Da Kuma Lalata Wani Wajen Kera Makaman Boko Haram


 

Sojojin runduna ta 7 na dakarun rundunar Operation Lafiya Dole sun sami nasarar kwato wasu mutane 85, mafiya yawansu mata da kananan yara, da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da su a arewacin jihar Borno, kan iyakan Tekun Chadi.

Yayin da yake sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau din nan Lahadi, kakakin rundunar sojin ta Nijeriya, Kanar Sani Usman Kukasheka, ya bayyana cewar an sami nasarar kwato mutanen ne sakamakon wani samame da sojojin suka kai garin Chukungudu mai matukar muhimmanci da nufin kakkabe sauran gyauron ‘yan Boko Haram din.

Kanar Kukasheka ya kara da cewa, hare-haren wadanda sojojin suka kai su daga shekaran jiya Juma’a zuwa jiya Asabar sun sami nasarar tsarkake garuruwan Bulankassa da Chukungudu da ake daukarsu a matsayin tungar ‘yan Boko Haram a yankin, yana mai cewa sojojin sun sami nasarar kashe wasu ‘yan ta’addan Boko Haram din su biyar da kuma tilasta wa wasu da dama ranta cikin na kare.

Kakakin sojin ya kara da cewa sojojin sun sami nasarar kwato wasu makamai da bama-bamai da manyan bindigogi da albarusai masu yawa, kamar yadda kuma sun gano wata masana’anta na kera bama-bamai a garin Geram inda ya ce sun sami wasu jigidoji da aka shirya su da nufin kai hare-haren kunar bakin wake, inda ya ce an tarwatsa wadannan wajaje na kera makaman, kamar yadda kuma ya ce rundunar sojan ta rasa sojanta guda yayin gumurzun.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like