Sojojin Saman Najeriya Ta Tabbatar Cewa Jiragen Yakinta Sun Hallaka Manyan Kwamandojin Boko Haram Uku
A wata Sanarwar da ya aikewa Sashin Hausa na Muryar Amurka, Kakakin sojojin saman Najeriyar ya ce an ga wasu gungun yan ta’adda sun tattaru a wani sansanonin dake Mantari bayan da wasu yan ta’adda suka zo cikin motocin yaki suna daf da kai hari.

Take kuma aka tada jiragen yaki inda suka afka musu a ka kuma aami nasarar hallaka wasu manyan kwamandojin na Boko haram uku wato QA’ID QA’ID da suka hada da Abba Tukur Maimusari da Bakura Jega

Kazalika bayan farmaki na farko da ya hallaka mayakan da dama daga bisani wasu mayakan sun dawo wannan sansanonin don debe gawawwakin mutanensu inda nanma jiragen yakin suka dawo suka kuma kara masu aman wuta. Kimanin dai zunzururutin matakan sama da Dari ne jiragen yakin suka hallaka.

Duka wannan kuma na zuwa ne a daidai Lokacin da manyan Hafsoshin kasa da na sama, Laftanar Janar Farouk Yahaya da Air Marshall Oladayo Amao ke ziyara a jihar Borno don yin Nikon kirsimati da dakarun dake bakin daga.

Kakakin sojojin saman yace Wani bayanin sittin da suka samu ya nuna yan ta’addan na shirin kai gari ne yayin da ake tsaka da bukukuwan kirsimati da na sabuwa shekara kana sun kuma tsara kawo cikas a babban zaben da za ai a shekara mai zuwa idan Allah ya kaimu.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like