Mutane 5 ne suka mutu inda wasu 12 suka jikkata sakamakon harin bam da jiragen yakin sojin Siriya suka kai a wasu unguwannin kasar.
Wani gini ya rushe gaba daya sakamakon harin. Jami’an taimako na kungiyoyin farar hula na ci gaba da aikin ciro mutane daga karkashin buraguzan ginin.
An kai wadanda aka jikkata zuwa asibitin yankin.