Sojojin Siriya sun kwace sansanin ‘yan tawaye


 

 

Rahotanni da ke fitowa daga Siriya, na cewa dakarun gwamnatin kasar sun yi nasaran kwace iko da sansanin Handarat dake arewacin Aleppo daga hannun ‘yan tawaye.

 

Birnin na Aleppo dai ya wayi gari da harin bama-bamai a kan manyan masana’antun burodi da ke garin Anadan da kuma daya a garin kafar Nahan. Wadannan hare-hare dai na ci gaba da haifar da fargaba ga tasirin sake shiga tattauna sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya. Da yake ganawa da shugaban darikar katolika a fadarsa da ke Batikan, manzon Majalisar Dinkin Duniya a Siriyar Staffan de Mistura, ya ce da kamar wuya a shawo hankalin dukkanin bangarori da ke lugujen wuta da juna su zauna teburin sulhu ganin yadda jiragen yakin gwamnati ke ci gaba da sake bama-bamai a yankuna da ‘yan tawaye ke rike da su.

Rahotannin kungiyoyin sa ido dai na cewa akalla mutane 298 ne suka gamu da ajalinsu tun bayan rushewar yarjejeniyar da kasashen Rasha da Amirka suka cimma a ranar 19 ga watan Satumba. Har yanzu dai, bayanai na cewa akalla mutane 300,000 ne fama da karancin abinci da magunguna da sauran kayan more rayuwa a birnin na Aleppo.

You may also like