Sojojin sun kama wasu motoci uku dake dauke da harsashi 300,000 a jihar Ogun


Rundunar sojin Najeriya ta kwace wasu motoci uku makare da dubban harsashai a yankin Igbogila-Ilara na jihar Ogun.

Enobong Udoh, shugaban rundunar sojan Najeriya ta 82 ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Lagos.

Udo, wanda ya samu wakilcin Olusegun Olatunde, ya ce sojoji sun kama motocin tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro.

Ya ce motocin da aka tsayar da su a kauyen Balogun suna dauke da harsashi da yawansu yakai 300,000.

Olatunde, ya ce jami’an tsaron sun cimma wannan nasarar ne bayan sirri da suka samu dake nuna cewa motocin suna dauke da harsashin.

Ya kara da cewa an boye harsashin ne cikin wani wuri na musamman da aka kera na katako inda aka rufe shi da karfe.

Direbobin sun ranta a na kare bayan da suka hangi jami’an tsaron.

You may also like