Sojojin kasar Turkiyya sun yi luguden wutan kan sansanoni 5 na haramtacciyar kungiyar PKK a garin Dağlıca na gundumar Yusekova da ke a jihar Hakkari.
Sun kai farmakai a wannan garin wanda yake a tsakanin duwatsun Aktutun da Ikiyaka ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuki.
Ababen hawan wadanda suka samu nasarar cika aikinsu sun dawo lamin lafiya ba tare da an samu wata matsala.
Gabanin wadannan hare-haren,Jiragen saman Turkiyya 2 sun gudanar wasu farmakai a yankin Cukurca na jihar Hakkari,inda suka kashe ‘yan ta’addar PKK 4.